Featured
Majalisar Wakilai Tana Goyon Bayan Shugaba Tinubu Akan Ciyo Bashi – Abbas

Majalisar Wakilai ta tabbatar da cikakken goyon bayanta game da yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke ciyo bashi, inda Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, ya ce bashi hanya ce ta samun kuɗaɗen da za su taimaka wajen gina muhimman ayyukan raya ƙasa. Ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin taron shekara-shekara karo na 8 na African Network of Parliamentary Budget Office (AN-PBO), inda ya karyata rahotannin da ke cewa majalisar ba ta goyon bayan kudirin gwamnati na ciyo bashi.
Abbas ya ce wasu rahotanni sun yi kuskuren fassara jawabin wani jagoran majalisar a wani taro na kasashen Yammacin Afirka, wanda hakan ya jawo zargin cewa Majalisar ba ta goyon bayan Tinubu akan batun ciyo bashi. Ya bayyana wannan labari a matsayin mai “ yaudara”, yana mai tabbatar da cewa Majalisar ta 10 da Majalisar Dattawa na marawa shirin bashi baya, domin cika bukatun raya kasa da tallafa wa talakawa.
Kakakin ya jaddada cewa, gwamnatin Tinubu tana mayar da hankali wajen amfani da kuɗaɗen bashin ne wajen manyan ayyuka masu amfani, kamar samar da wutar lantarki, harkokin sufuri da noma domin ƙara haɓaka hanyoyin samun kuɗin shiga ga ƙasar. Ya ce wannan tsarin zai zama ginshiƙi wajen haɓaka tattalin arziki da rage talauci, tare da ƙarfafa kulawar majalisa a kan yadda kuɗin za su kasance an tafiyar da su yadda ya kamata.
Abbas ya kuma bayyana cewa Najeriya tana asarar kusan dala biliyan 18 a duk shekara sakamakon rashawa da haramtattun kudaden fita daga ƙasa. Saboda haka, ya ce shirin ɗaukar bashi da aka tsara bisa ka’ida, tare da tsauraran matakai na yaki da rashawa, shi ne hanya mafi dacewa don kare makomar tattalin arziƙin ƙasa.