Featured
Abun Al’ajabin Zazzau Ya Janye Daga Neman Takarar Majalisar Wakilai

Ɗantakarar majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar mazaɓar Sabon Garin Zariya a jam’iyyar APC, Mahmud Sadis Buba wanda aka fi sani da Abun Al’ajabin Zazzau, ya sanar da janye takararsa nan take.
A cikin wata wasiƙa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki, shugabannin APC da kuma iyalai da abokan arziki. Ya ce matakin na da nasaba da tabbatar da haɗin kai a cikin jam’iyyar.
Abun Al’ajabin Zazzau ya bayyana cewa haɗa kai ƙarƙashin ɗantakara ɗaya ne zai taimaka wajen samun nasara ga APC da kuma ci gaban mazaɓarsa da jihar bakiɗaya. A makon da ya gabata ne aka tantance shi domin takarar, sai dai daga baya aka fara taƙaddama kan shekarunsa a kafafen sada zumunta.