Featured
Ƴan Sanda Sun Bankaɗo Badaƙalar Naira Biliyan 4.8 a Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Kainji

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja ta cafke mutane 14 da ake zargi da hannu a wasu manyan laifuka biyu, wadanda su ka hada da sata da kuma lalata kayan aikin a tashar samar da wutar lantarki ta Kainji Power Plant, wanda darajarsu ta kai sama da Naira biliyan 4.8, da kuma wani shirin yin garkuwa da kai na karya domin karɓar kudin fansa Naira miliyan 7. Hukumar ta ce binciken ya fara ne bayan kamfanin Mainstream Energy Solutions Ltd ya shigar da ƙorafi a ranar 11 ga Agusta, 2025, inda aka gano wani dogon shirin sata da ma’aikatan tsaro na tashar ke yi.
Binciken ya nuna cewa an sace wasu manyan karafunan tashar kuma aka sare su aka sace tsawon lokaci tun 2023. An fara kama masu kula da wajen su biyu, Shaibu Abu Sufyan (35) da Ibrahim Musa (31), inda daga baya suka bayyana sunayen wasu jami’an tsaro goma da suke tare da su wajen satar. Sun haɗa da Zayyanu Musa, Jibrin Abdullahi, Hassan Musa, Micah Adamu, Attahiru Umar, Abdulrahman Usman, Ismaila Ibrahim, Mubarak Husseini, Adamu Abubakar da Abdullahi Abubakar (Zuma).
‘Yan sanda sun kuma gano cewa wannan rukuni yana haɗin guiwa da ‘yan sayen ƙarfen gwangwan su uku – Musa Khalid, Abah Khalid da Abdullahi na Nasarawa a Mashegu LGA – waɗanda ke kawo manyan na’urorin yankan ƙarfe a dare, su sare su, su ɗauka da manyan motoci. Bugu da ƙari, an gano mu’amalar Naira miliyan 12.5 tsakanin Abu Sufyan da ɗaya daga cikin ‘yan kasuwar, da kuma miliyan 11.5 a kan Ibrahim Musa. An ce an sayar da kayan satar ga kamfanoni a Lagos, Kwara da Osun.