Connect with us

Featured

Ƴan Sanda Sun Kama Wani Malamin Makarantar Allo Bayan Ya Zane Ɗalibinsa a Bauchi

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Bauchi ta kama wani malamin makarantar allo mai shekaru 28, Lawal Nasiru, bisa zargin daure ɗalibinsa da igiya tare da yi masa dukan tsiya. Rahotanni sun bayyana cewa yaron da aka gani, Sa’id Sani, mai shekaru 11, ya samu munanan raunuka a hannaye da ƙafafunsa sakamakon dukan da aka yi masa da sanda, sannan aka daure shi da igiya a ƙaramar hukumar Darazo ta jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakil, ya ce lamarin ya faru ne ranar 21 ga Satumba, 2025, inda wani mai suna Idris Mohammed mai shekaru 50 daga Gidan Waya, Darazo, ya kai korafi ofishin ‘yan sanda. Rundunar ta ce DPO na yankin, SP Auwalu Ilu, ya jagoranci jami’ansa suka kama wanda ake zargi kuma suka kai yaron asibitin gwamnati na Darazo domin duba lafiyarsa.

A lokacin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, yana mai cewa ya daure yaron ne saboda yunkurin tserewa daga makarantar allo kafin zuwan iyayensa. Sai dai yaron ya bayyana cewa an daure shi ne da igiya mai kauri na tsawon lokaci kuma aka ci gaba da dukansa.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin a mayar da shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na jihar domin gudanar da cikakken bincike. Rundunar ta tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargi a kotu da zarar an kammala bincike.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet