Featured
Ban Taɓa Tsammani Buhari Ba Zai Kawo Ƙarshen Boko Haram Ba – Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ƙungiyar Boko Haram ta taɓa zaɓar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin wakilinta domin shiga tattaunawa da gwamnatin tarayya a zamanin mulkinsa. Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin ƙaddamar da littafin “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum”, wanda tsohon babban hafsan tsaron ƙasa, Janar Lucky Irabor ya rubuta, a birnin Abuja.
Jonathan ya ce gwamnatin sa ta kafa wani kwamiti na musamman domin fara tattaunawa da kungiyar Boko Haram a lokacin da hare-haren ta ke ƙaruwa a arewacin ƙasar. A cewarsa, cikin mamaki ne suka gano cewa kungiyar ta zaɓi Buhari a matsayin wakilinta a tattaunawar, abin da ya nuna cewa akwai yuwuwar samun sulhu idan an ci gaba da yunƙurin.
“Tunda har suka zaɓe shi a matsayin wakili, sai na yi tunanin cewa da zarar ya hau mulki zai kawo ƙarshen matsalar,” in ji Jonathan kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Ya ce wannan dalili ne ya sa ya ji daɗin wannan zaɓi, yana ganin hakan na iya zama matakin kawo ƙarshen rikicin.
Sai dai tsohon shugaban ya nuna takaici cewa duk da shigowar Buhari mulki a 2015, har yanzu matsalar Boko Haram ba ta ƙare ba. Ya ce an yi tsammanin gwamnati za ta ci gaba da tattaunawar da aka fara domin samar da zaman lafiya, amma rikicin ya ci gaba da jawo asarar rayuka da ta dukiya a sassa da dama na ƙasar.