Featured
Farfesa Mahmood Yakubu Ya Sauka Daga Muƙamin Shugaban INEC
Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya sauka daga muƙaminsa bayan kusan shekaru goma yana jagorantar hukumar. A yayin taron da ya gudanar da kwamishinonin hukumar a shelkwatar INEC da ke Abuja ranar Talata, Farfesa Yakubu ya bayyana cewa ya mika ragamar shugabancin hukumar ga babbar kwamishina, May Agbamuche, wadda za ta riƙe mukamin shugaba a matsayin riko har zuwa lokacin da za a naɗa sabon shugaban hukumar.
May Agbamuche ita ce babbar kwamishinar da ta fi kowa dadewa a hukumar, lamarin da ya sanya ta zama zababbiyar wucin gadi don ci gaba da tafiyar da harkokin hukumar. Farfesa Yakubu ya bukaci kwamishinoni da daraktoci su bai wa Agbamuche cikakken goyon baya domin tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan hukumar cikin nasara a wannan lokaci na sauyin jagoranci.
Farfesa Mahmood Yakubu ya hau karagar shugabancin INEC ne a watan Oktoba 2015, bayan tsohon Shugaban Najeriya, Marigayi Muhammadu Buhari, ya naɗa shi don maye gurbin Farfesa Attahiru Jega. A shekarar 2020 kuma, Buhari ya sake tabbatar da nadin Yakubu a karo na biyu, domin ci gaba da jagorantar hukumar a wa’adi na biyu.
A lokacin jagorancinsa, Farfesa Yakubu ya jagoranci gudanar da manyan zaɓukan ƙasa biyu — na shekarar 2019 da 2023 — tare da zama ɗaya daga cikin shugabannin INEC mafi dadewa a tarihin Najeriya. Saukarsa daga muƙami na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran shugaban ƙasa zai naɗa sabon shugaban hukumar domin jagorantar shirye-shiryen zabukan gaba.
