Connect with us

Featured

MDCN Ta Gargadi Sabbin Likitoci Kan Amfani Da Fasahar AI

Hukumar Kula da Ayyukan Likitoci da Likitocin Haƙora ta Najeriya (MDCN) ta gargadi sabbin likitoci da kada su dogara sosai da fasahar Artificial Intelligence (AI), tana mai cewa ba za ta taɓa maye gurbin tunani, tausayi da mu’amala ta ɗan adam ba — waɗanda su ne ginshiƙan aikin likitanci. Babbar Sakatariya kuma Shugabar Hukumar, Farfesa Fatima Kyari, ce ta yi wannan gargadi a ranar Litinin 06 ga Oktoba, yayin bikin rantsar da sabbin likitoci 65 daga Jami’ar PAMO University of Medical Sciences, Port Harcourt.

Farfesa Kyari ta ja hankalin sabbin likitocin cewa ko-da-yake suna cikin zamanin AI, bai kamata su manta cewa na’ura ba ta da motsin rai ko ikon yin hukunci na ɗabi’a kamar ɗan adam ba. Ta ƙara da cewa nasarar aikin likita ba ta ta’allaka ga ilimin kimiyya kaɗai ba, har ma da kulawa da tausayi ga marasa lafiya. “Ku tuna, likitanci ba kawai da alkalami ake yi ba —har da hannu da zuciya,” in ji ta.

A nasa jawabin, tsohon Gwamnan Jihar Rivers kuma Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Jami’ar PAMO, Dakta Peter Odili, ya yaba da ci gaban da jami’ar ta samu cikin ƙasa da shekaru takwas, inda ta samar da sama da ƙwararrun ma’aikatan lafiya 330. Ya kuma bai wa kowane sabon likita kyautar Naira 100,000 tare da kiran gwamnatin tarayya ta duba batun albashi da jin daɗin likitoci domin rage yawaitar barin ƙasa da suke yi.

Tun da farko, Mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Smith Jaja, ya bayyana cewa sabbin likitocin su ne rukuni na farko da suka kammala karatu da jarrabawa a asibitin koyarwa na jami’ar. Ya bayyana su a matsayin ƙwararru masu jajircewa wajen kare mutunci da ɗabi’un aikin likitanci a Najeriya da ma wajen ƙasar.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet