Featured
Inspector Ya Harbe Abokin Aikinsa Har Lahira

Wani Inspector na ’Yan Sanda mai suna Victor Okus ya harbe abokin aikinsa, Ibrahim Sani, har lahira a birnin Port Harcourt na Jihar Rivers, yayin da wani jami’i, Daniel Dauda, ya tsira da raunukan harbin bindiga. Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a wani babban kantin sayar da kaya da ke yankin Trans-Amadi.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an suna bakin aiki tare da sojoji lokacin da lamarin ya faru, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna yankin. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da cewa an garzaya da waɗanda aka harba asibiti, inda Ibrahim Sani ya rasu, yayin da Daniel Dauda ke karɓar magani.
Rundunar ’yan sandan Rivers ta ce an kama wanda ake zargi kuma yana tsare a hannun ’yan sanda, yayin da Kwamishinan ’yan sandan jihar ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike. Rundunar ta jaddada cewa za a gurfanar da wanda ake zargi gaban kotu, tare da jan hankalin jami’ai kan muhimmancin kula da makamai yayin aiki.