Featured
Gwamnan Rivers Ya Kori Dukkan Kwamishinoninsa

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya tsige dukkan kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnati da ke cikin gwamnatinsa, bisa umarnin da ya biyo bayan hukuncin Kotun Koli. Kakakin yada labaran gwamnan, Nelson Chukwudi, ya sanar da hakan a cikin wata takarda da aka fitar a Fatakwal ranar Laraba 01 ga Oktoba, inda ya ce matakin ya fara aiki nan take.
Fubara ya bayyana wannan ne yayin wani taron bankwana da majalisar zartarwarsa domin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai. A wajen taron, ya gode wa tsoffin kwamishinonin bisa gudummawar da suka bayar ga ci gaban jihar cikin shekaru biyu da suka gabata.
Haka kuma, gwamnan ya yi kira ga ’yan Najeriya da su haɗa kai da shugaban ƙasa wajen gina ƙasa mai zaman lafiya, tsaro da cigaba, tare da tabbatar da makoma mai kyau ga al’umma. Ya kara da cewa yana da niyyar ci gaba da gudanar da mulki da ƙwarin gwiwa, tare da godewa mutanen Rivers bisa goyon bayan da suke ba shi.
A baya-bayan nan, tsohon gwamnan riko na jihar, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (ritaya), ya dakatar da kwamishinonin Fubara da sauran jami’an gwamnati a lokacin da aka kafa dokar ta-baci a jihar. Tun bayan barin sa ofis a ranar 18 ga Satumba, makomar wadannan mukarraban Fubara ta kasance cikin rudani, lamarin da ya sa majalisar dokokin jihar ta bukaci gwamnan ya gabatar da sabbin sunayen kwamishinoni domin tantancewa tare da kasafin kudin 2025.