Connect with us

Featured

Ƴan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa da Mutane a Bauchi

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Bauchi ta kama wasu mutum shida da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da kubutar da mutane uku da aka sace daga ƙauyen Euga da ke ƙaramar hukumar Toro. Kakakin rundunar, SP Ahmed Wakil, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba 15 ga Oktoba, inda ya ce an gudanar da samamen ne bayan samun kiran gaggawa daga wani mazaunin yankin a ranar 29 ga Satumba, 2025.

Wakil ya ce bayan rahoton, jami’an rundunar daga Toro Area Command, sashen ‘yan sanda na Toro da Nabordo tare da taimakon masu tsaron yankin, sun gudanar da aikin haɗin gwiwa wanda ya kai ga gano maboyar masu garkuwa a wajen garin da kuma ceto waɗanda aka sace ba tare da wata matsala ba.

An bayyana sunayen waɗanda aka kama da suka haɗa da Abubakar Usman, Adamu Alo, Abubakar Aliyu, Umar Habu, Abubakar Mamman Abubakar, da Shehu Sambo. Wakil ya ce waɗanda aka ceto sun koma wurin iyalansu cikin koshin lafiya, yayin da bincike ke ci gaba don gano cikakkun bayanan lamarin.

Kakakin ya ƙara da cewa wadanda ake zargi sun fara ba da muhimman bayanai ga jami’an bincike, kuma za a mika su ga sashen yaki da garkuwa da mutane don ƙarin bincike da gurfanarwa a kotu. Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yaba da jajircewar jami’an, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai masu amfani don taimaka wa wajen yakar laifuka.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet