Addini
Hisbah Ta Fara Shirye-shiryen Ɗaura Auren Maiwushirya Da Ƴarguda

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa ta fara shirye-shiryen ɗaura aure tsakanin sanannun masu amfani da TikTok, Ashiru Idris (Maiwushirya) da Basira (Ƴarguda), bisa umarnin da wata kotun majistare ta bayar. Wannan na zuwa ne bayan kotun ta gano cewa bidiyoyin da suke wallafawa a shafukansu suna nuna kusanci da alamar soyayya tsakaninsu.
A ranar Litinin, kotun majistare da ke Kano ta bai wa hukumar Hisbah umarnin gudanar da auren cikin wani lokaci da ta kayyade, bayan da aka gurfanar da matasan biyu a gabanta bisa zargin yaɗa bidiyoyin rashin ɗa’a a shafukan sada zumunta.
Mai shari’a Halima Wali, wadda ta jagoranci zaman kotun, ta bayyana cewa matasan sun saba da dokokin tarbiyya ta jama’a da kuma ɗabi’un al’ummar jihar, saboda haka kotun ta yanke hukuncin cewa ya zama dole a ɗaura auren don kaucewa sake aikata irin waɗannan abubuwan a gaba.
Kotun ta kuma gargadi hukumar Hisbah da matasan cewa rashin gudanar da auren a cikin lokacin da aka ƙayyade zai zama saɓa wa umarnin kotu, wanda zai iya janyo hukunci mai tsanani ga ɓangarorin da abin ya shafa.