Featured
Tinubu Ya Bayyana Kwankwaso A Matsayin Mutum Mai Son Ci Gaba

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin abokin tafiya da ke cikin sahun ’yan ra’ayin ci gaba, duk da cewa ya bar jam’iyyar APC. A sakon taya murna da ya aikawa Kwankwaso a ranar zagayowar haihuwarsa ta 69, Tinubu ya yaba da rawar da tsohon gwamnan Kano ya taka a ci gaban ƙasa da irin jajircewarsa wajen hidimar jama’a.
A cewar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai da dabarun mulki, Bayo Onanuga, Tinubu ya taya iyalai, abokai da magoya bayan Kwankwaso murnar wannan rana ta musamman. Ya ce a matsayinsa na tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai a jamhuriya ta uku, tsohon ministan tsaro, da kuma gwamna na Kano har sau biyu, Kwankwaso ya bayar da gagarumin gudunmawa ga ci gaban ƙasa.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa tasirin siyasar Kwankwaso a Arewacin Najeriya, musamman a Kano, ya nuna irin kishin talaka da manufofin siyasa da suka yi kama da na marigayi Malam Aminu Kano da Alhaji Abubakar Rimi. Ya ƙara da cewa su biyun sun yi aiki tare a majalisar tarayya a shekarar 1992, sannan daga baya suka shugabanci jihohinsu a 1999, kuma sun yi haɗin gwiwa wajen kafa jam’iyyar APC.
Tinubu ya ce duk da cewa Kwankwaso daga baya ya bar APC ya kafa jam’iyyar NNPP, hakan bai cire shi daga cikin ’yan ra’ayin ci gaba ba. Shugaban ƙasa ya yi masa fatan alheri, lafiya da ƙarin shekaru masu albarka don ci gaba da bauta wa ƙasa da jama’a.