Connect with us

Featured

Ba Wanda Ya Isa Ya Rabani Da Kwankwaso — Gwamna Abba

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karyata jita-jitar da ke cewa akwai sabani tsakaninsa da jagoransa na siyasa, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin bikin taya Kwankwaso murnar cika shekara 69 da haihuwa, wanda aka gudanar a Madobi ranar Talata 21 ga Oktoba, inda ya jaddada cewa ba wanda zai iya raba shi da Kwankwaso.

Gwamna Abba ya ce wasu mutane na ƙoƙarin haifar da rikici tsakaninsa da jagoransu, amma duk irin wannan yunƙuri ba zai yi nasara ba. Ya bayyana cewa zai ci gaba da bin tafarkin Kwankwasiyya da bin ka’idar da Kwankwaso ya kafa, yana mai cewa, “Kwankwaso shugaba ne da Allah ya ba mu.”

Ya kuma yi addu’a ga Allah ya ƙara wa Kwankwaso lafiya da tsawon rai, yana bayyana shi a matsayin shugaba mai hangen nesa wanda jagorancinsa ke ci gaba da haskaka tafiyar siyasar jihar Kano da jam’iyyar NNPP.

Wannan jawabi na Gwamna Abba ya kawar da jita-jitar da ta dade tana yawo cewa akwai sabani tsakaninsa da jagoransa, bayan bullar wani rukunin “Abba Tsaya da Kafarka” da ake zargin yana neman ƙarin ikon mulki ga gwamnan. Jawabin nasa ya tabbatar da cewa haɗin kan Kwankwasiyya yana nan daram a jihar Kano.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet