Featured
2027: Kwankwaso Ba Zai Zama ‘Spare Tyre’ a Gwamnatina Ba — Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa zasu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, idan suka yi nasara a zaben shugaban kasa na 2027. Obi ya bayyana hakan ne yayin da ya gabatar da Kwankwaso a matsayin wanda ya zaba a matsayin mataimakinsa a taron jam’iyyar da aka gudanar a Abuja.
Obi ya ce gwamnatinsu za ta kasance mai dogaro da tuntubar juna, hadin kai da raba nauyin jagoranci, yana mai jaddada cewa mukamin mataimakin shugaban kasa ba zai zama na ado ko “spare tyre” ba. Ya ce dukkan manyan shawarwari za a rika daukarsu ne tare da tuntubar juna a matsayin abokan aiki masu matsayi daya.
Bayan karbar takararsa a hukumance, Obi ya gayyaci Kwankwaso ya kasance abokin takararsa, yana mai cewa suna da irin wannan hangen nesa musamman a bangarorin ilimi, tsaro da samar da dama ga kowa. Ya ce zai hada kai da Kwankwaso domin tabbatar da wadannan manufofi idan suka samu damar jagorantar kasar.