Connect with us

Featured

Ƙarin Kashi 15% Na Harajin Man Fetur Zai Jefa Ƴan Najeriya Cikin Mawuyacin Hali – ADC

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya janye kudirin da ya amince da shi na kakaba harajin shigo da mai (petrol da dizal) har kashi 15%, tana cewa matakin rashin tausayi ne da zai kara tsananta halin kuncin tattalin arziki da ake ciki. Kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa tsarin gyaran tattalin arzikin gwamnatin Tinubu bai nuna damuwa da halin da talakawa ke ciki ba, inda ya ce duk wani ci gaban tattalin arziki da sai yan Najeriya sun wahala sannan ya samu, wannan ci gaba ne mara amfani.

ADC ta yi Allah-wadai da wannan haraji da gwamnatin ta ce an kaddamar domin kare masana’antun tace mai na cikin gida da daidaita harkar kasuwancin man fetur. Sai dai jam’iyyar ta ce wannan tsarin zai iya tura farashin litar man fetur zuwa sama da N1,000, abin da zai kara radadin rayuwa ga iyalai, manoma, ‘yan kasuwa da direbobi da ke fama da hauhawar farashi bayan cire tallafin mai da durkusar da naira.

Jam’iyyar ta kuma caccaki gwamnatin APC da cewa tana tafiyar da tattalin arzikin kasa cikin rudani da son rai, ba tare da tsarin da ke kare bukatun al’umma ba. Ta kuma nuna rashin jin dadi kan yadda matatar mai ta Fatakwal ta sake lalacewa bayan an kashe dala biliyan 1.5 wajen gyaranta, abin da ya haifar da asarar N366.2 biliyan.

A karshe, ADC ta bukaci gwamnati da ta janye wannan haraji nan take, tana mai gargadi cewa idan ba a yi hakan ba, zai iya haifar da karin matsin tattalin arziki da bacin rai a tsakanin jama’a. Ta jaddada cewa kafin gwamnati ta sanya irin wannan haraji, dole ne ta tabbatar da ingantacciyar saka jari a cikin matatun cikin gida domin samar da wadataccen mai a kasar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet