Featured
Gwamnatin Tarayya Za Ta Biya Likitoci Naira Biliyan 11.9

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na sakin Naira biliyan 11.995 cikin awanni 72 domin biyan bashi ga likitoci da sauran ma’aikatan lafiya a Najeriya. Wannan mataki na zuwa ne a yayin da likitoci ƙarƙashin kungiyar NARD ke ci gaba da yajin aikin kasa baki ɗaya saboda rashin biyan hakkokinsu da matsalolin yanayin aiki.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar Lafiya ta fitar, ta bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu ta ɗauki matakai masu ƙarfi wajen tabbatar da kwanciyar hankali da walwalar ma’aikatan lafiya, ciki har da biyan bashin albashi, tallafin kayan aiki, da kuma ɗaukar sabbin ma’aikata domin rage ƙarancin likitoci. A cewar sanarwar, biyan bashin watanni bakwai na karin albashi ya riga ya fara, kuma wannan sabon kuɗi zai biya sauran hakkoki da suka rage.
Gwamnatin ta ce ta bayar da waiver na musamman domin ɗaukar sabbin ma’aikata a asibitocin tarayya, musamman bayan barazanar “brain drain” da ke barazana ga tsarin kiwon lafiya. A shekarar 2024 an ɗauki ma’aikatan lafiya fiye da 20,000, kuma a 2025 ana cigaba da ɗaukar wasu 15,000. Haka kuma, gwamnatin ta riga ta biya biliyan 610.6 a matsayin kudin horon likitoci masu yin karatun ƙwarewa (MRTF).
Sai dai duk da waɗannan matakai, NARD ta ce ta shiga yajin aiki ne saboda rashin cika yarjejeniyoyi da gwamnatin ta yi a baya. Shugaban kungiyar, Dr. Mohammad Suleiman, ya ce matakin bai da nasaba da siyasa ko son kai, amma yunkuri ne na kare tsarin kiwon lafiya da ke rushewa. Ya ce likitoci a ƙasar suna fama da ƙarancin albashi, gajiyawa, da rashin kayan aiki, abin da ke rage ingancin kula da marasa lafiya.