Featured
Tinubu Ya Sake Naɗa Marwa a Matsayin Shugaban NDLEA

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nada tsohon kwamandan soja, Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (rtd), a matsayin shugaban Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) na wani sabon wa’adi na shekaru biyar. Wannan na zuwa ne bayan kammala wa’adinsa na farko da ya fara a 2021, lamarin da zai cigaba da riƙe madafun iko a hukumar har zuwa shekarar 2031.
Marwa, wanda ya taba zama shugaban kwamitin kawar da yawan shan miyagun ƙwayoyi daga 2018 zuwa 2020, na da dogon tarihin aiki a rundunar sojin Najeriya da kuma ƙwarewa a harkokin diflomasiyya. Ya yi karatun digiri na biyu a Jami’ar Pittsburgh da Harvard, tare da rike muhimman mukamai kamar ADC ga tsohon COS, Janar T.Y. Danjuma, da kuma wakilin tsaro a Washington DC da Majalisar Ɗinkin Duniya.
Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa hukumar ta samu gagarumin ci gaba a ƙarƙashin jagorancin Marwa, ciki har da cafke sama da mutum 73,000 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, da kwace tan-tan na nau’o’in ƙwayoyi sama da miliyan 15. Haka kuma NDLEA ta jagoranci manyan yaƙe-yaƙe da wayar da kai kan illolin shaye-shaye a faɗin ƙasar.
Shugaba Tinubu ya jinjinawa Marwa bisa ƙoƙarinsa, yana mai cewa sake naɗinsa hujja ce ta amincewa da kokarin da yake yi domin magance barazanar shaye-shaye musamman tsakanin matasa. Yanzu dai tsohon gwamnan Lagos da Borno zai fuskanci sabon nauyi na ƙarfafa nasarorin da ya samu a wa’adinsa na farko.