Featured
Zangona Na Biyu Zai Zama Mafi Tsanani Ga Dillalan Ƙwaya – Marwa

Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (rtd.), ya sake aika gargaɗi mai tsanani ga manyan barayin miyagun ƙwayoyi da masu safarar su, yana mai cewa zangon aikinsa na biyu zai kasance mafi tsauri. Marwa, wanda Shugaba Bola Tinubu ya sake naɗawa don yin wa’adin shekaru biyar na biyu, ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi wa ma’aikatan NDLEA da suka tarbe shi da murna a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
A cikin jawabin, Marwa ya ce an ba shi sabon kuzari da goyon bayan gwamnati don ci gaba da yaƙi da miyagun ƙwayoyi ba tare da sassauci ba. Ya ce wannan lokaci “shi ne mafi dacewa” ga duk masu harkar fataucin kwayoyi su daina aikata laifi su koma halastacciyar hanyar samun abin yi. Ya ƙara da cewa duk wanda ya ƙi bin doka zai gamu da kamawa, kwace kayan laifi, take masa dukiya, sannan a tura shi gidan yari ya dawo ba tare da komai ba.
Marwa ya kuma jaddada cewa NDLEA za ta ci gaba da zama tsoro ga ƙungiyoyin safarar miyagun ƙwayoyi, yana tuna cewa tun ranar da ya hau kujerar shugaban hukumar ya bayyana manufarsa ta karya wannan gungun. Ya yabawa goyon bayan manyan jami’an gwamnati da abokan hulɗar ƙasa da ƙasa, waɗanda suka taimaka wajen ƙoƙarin da hukumar ke yi na kawar da miyagun ƙwayoyi a Najeriya.
A gefe guda, ya sanar da faɗaɗa cibiyoyin jinya da gyaran dabi’u na NDLEA, inda ya bayyana cewa hukumar za ta ƙara cibiyoyi bakwai a kasafin kuɗin 2025 don tabbatar da cewa kowace jiha na da nata cibiyar. Har ila yau, ya yaba wa Ma’aikatar Lafiya da Ta Ilimi bisa amincewa da shirin yin gwajin miyagun ƙwayoyi ga ɗaliban da za a karɓa a manyan makarantu, yana mai cewa wannan zai taimaka wajen gano matsalar tun kafin ta rikide zuwa jaraba.