Featured
Sunusi Lamido Ne Halastaccen Sarkin Kano – Rabi’u Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sake jaddada cewa Muhammadu Sanusi II shi ne sarkin Kano na gaskiya da gwamnati da al’ummar jihar ke amincewa da shi. Kwankwaso ya yi wannan furuci ne yayin bikin yaye dalibai karo na huɗu na jami’ar Skyline University a Kano, inda ya ce duk wani da aka nada daga wajen jihar ba shi da ingantacciyar hujjar zama sarki.
Ya kuma yabawa jami’ar bisa ci gaba da jajircewa wajen samar da ingantacciyar ilimi, tare da taya daliban da suka kammala karatu murna, musamman ganin cewa sama da kashi 60 cikin ɗari mata ne suka yi nasarar kammala. Ya gargadi matasa maza da su dage da karatu domin kada su bar mata su zarce su a fannin ci gaban ƙasa.
A bangaren tsaro, Kwankwaso ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta dakile hare-haren da ’yan bindiga ke yi daga jihar Katsina suna shigowa karamar hukumomi irin su Tsanyawa, Shanono, Gwarzo da Karaye. Ya ce matsalar tsaro ta fara daga Zamfara ta bazu zuwa Sokoto, Kebbi, Kaduna kuma yanzu tana barazana ga Kano da Jigawa.
Shi ma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wanda shi ne Chancellor na jami’ar, ya shawarci sabbin ɗaliban da su rike gaskiya da aiki tukuru, yana mai cewa ilimi ba takardar shaidar kammala karatu ba ce, illa tasirin da mutum ke yi ga al’umma. Jami’ar ta bayyana cewa dalibai 24 sun samu sakamako matuƙar kyau (First Class) cikin dalibai 180 da suka kammala, tare da bayar da digirin babbar makaranta (postgraduate) a karon farko tun kafa ta.