Featured
Gwamnatin Sokoto Ta Tabbatar Da Ɓarkewar Cutar Amai Da Gudawa a Faɗin Jihar

Gwamnatin jihar Sokoto ta fara aikin gaggawa bayan bullar cutar amai da gudawa (cholera) a kananan hukumomi 12 na jihar. Cutar ta bayyana ne a farkon makon nan, lamarin da ya sa hukumomin lafiya suka yi hanzarin tura jami’ai da kayayyakin agaji cikin gaggawa zuwa cibiyoyin kiwon lafiya da abin ya shafa.
Jami’in Ma’aikatar Lafiya ta jihar, Biliyaminu Sifawa, ya ce an tura ma’aikatan lafiya zuwa asibitoci cikin awa 24 da samun rahoton bullar cutar. Ya ce jami’an sun tabbatar da kula da marasa lafiya da samar da magunguna da sauran kayan kariya domin dakile yaduwar cutar cikin sauri.
Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tallafa da kayayyaki da suka hada da kwalaye 20 na Aqua Tabs, magunguna 577 na kula da cholera, WASH dignity kits 289, ganguna shida na sinadarin chlorine, da sauran muhimman kayan aikin gaggawa. UNICEF ta ce kayayyakin sun kai ga dukkan kananan hukumomin da abin ya shafa, ciki har da Binji, Gada, Goronyo, Wamakko da Sokoto North da South.
Rahotanni sun nuna cewa jihar Sokoto da wasu jihohin Arewa maso Yamma na yawan fuskantar cholera musamman a damina, sakamakon rashin tsaftar ruwa da bude bayan gida. Hukumar lafiya ta jihar ta ce tana cigaba da sa ido da kula da al’umma, tare da wayar da kai kan tsaftar muhalli da tsaftar ruwa domin dakatar da karin yaduwar cutar.