Connect with us

Featured

Kabiru Turaki Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar PDP

Dr. Kabiru Turaki (SAN) daga jihar Kebbi ya lashe zaben shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa a babban taron zaben da aka gudanar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo. Turaki ya samu kuri’u 1,516, inda ya doke abokin takararsa Garuba Lado wanda ya samu 41. A cewar kwamitin gudanar da taron, jimillar wakilai 3,141 ne suka hallara, 2,745 aka tantance, yayin da kuri’u 275 suka lalace.

Sakataren kwamitin taron, Sanata Ben Obi, ya bayyana cewa wasu kujeru 17 an yi takara kansu ne ba tare da hamayya ba, lamarin da ya tabbatar da Sauarin Adekunle ya zama Mataimakin Sakataren Tsare-Tsaren Jam’iyya. Turaki, wanda ya taba zama minista a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya gaji shugabancin jam’iyyar a wani lokaci da ake ganin PDP na fuskantar manyan ƙalubale.

A jawabinsa na karɓar aiki, Turaki ya yi alkawarin kawo ƙarshen abin da ya kira zalunci da murɗa wa al’umma kai, yana mai cewa za su buɗe kunnen su su saurari mambobi domin gudanar da jam’iyya bisa adalci, gaskiya, da daidaito. Ya ce sabon shugabanci ba zai yi watsi da amana ba, kuma zai tabbatar da bin muradun ‘yan jam’iyya da jama’a.

Ya bayyana cewa PDP na fuskantar matsayi mai sarkakiya, amma sabon shugabanci ya shirya tsaf don gyara martabar jam’iyyar. Turaki ya ce za su fara ziyartar manyan jiga-jigan jam’iyyar da suka fusata ko suka bar PDP, domin dawo da su a ƙoƙarin “ceton dimokuraɗiyyar Najeriya daga rugujewa.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet