Featured
INEC za ta bayyana matsayarta kan makomar takarar Pantami, Nami da Adamu

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) za ta bayyana matsayinta a yau Talata kan makomar wasu ’yan takarar jam’iyyun siyasa, bayan hukuncin Kotun Ƙoli da ya tabbatar da ingancin sashe na 77 da 84 na Dokar Zaɓe ta 2026.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, zai yi wa manema labarai jawabi a wani taron manema labarai, inda ake sa ran zai yi bayani kan shirye-shiryen hukumar na zaɓen 2027 da kuma makomar ’yan takarar da hukuncin Kotun Ƙoli ya shafa.
Read Also : Gov. Buni Mourns Twin Doctors, Sends High-Powered Delegation to Bereaved Family
A Gombe, ana nuna damuwa kan makomar Farfesa Isa Ali Pantami, bayan ya janye daga takarar gwamnan APC a ranar 19 ga Mayu, ya yi murabus daga jam’iyyar sannan ya koma PDP. Sai dai wani jigo a PDP ya ce hukuncin Kotun Ƙoli bai tabbatar da cewa sunan Pantami ba ya cikin kundin rajistar PDP ba.
Haka kuma, ana fuskantar tambayoyi kan Muhammad Nami, ɗan takarar PDP na gwamnan jihar Neja, da kuma tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu, wanda ya maye gurbin ɗan takarar SDP a Nasarawa. INEC ta tsara fitar da jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar gwamna da Majalisar Jiha a ranar 10 ga Oktoba 2026.
Pingback: Babban Sakataren Majalisar Ƙoli Kan Shari’ar Musulunci a Najeriya Ya Rasu - KAKAKI 24