Connect with us

Featured

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Hukuncin Kisa Ga Masu Garkuwa Da Mutane

Majalisar Dattawa a Najeriya ta ɗauki mataki mai tsauri kan tabarbarewar tsaro, inda ta ayyana garkuwa da mutane a matsayin ta’addanci tare da ba da shawarar hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin ba tare da damar rage hukunci ko tara ba. Matakin ya biyo bayan harin da aka kai cocin Christ Apostolic Church a Eruku, ƙaramar hukumar Ekiti ta jihar Kwara, ranar 18 ga Nuwamba, inda ’yan bindiga suka kashe mutane biyu suka yi garkuwa da wasu 38 da daga bisani jami’an tsaro suka ceto. Sanatoci sun ce wannan lamari ya nuna yadda matsalar ta’addanci ke ci gaba da bazuwa zuwa Kudancin ƙasar, tare da raunana tsaron karkara da al’umma.

Sanata Yisa Ashiru daga Kwara, wanda ya gabatar da kudirin gaggawa, ya bukaci inganta dabarun tsaro, ganin yadda hare-haren da suka hada da sace dalibai. Sanata Issa Jibrin daga Kogi ya yi kashedi kan karancin jami’an tsaro a kasar, yana mai cewa duka rundunonin soja, ’yan sanda da hukumomin tsaro ba su kai mutum miliyan daya ba, lamarin da ya ce ya bukaci karin kayan aiki, dabarun leken asiri da kafa rundunar tanadi. Haka kuma an koka kan yadda hare-haren ke matsowa kusa da Osun ta bangaren Ekiti, inda aka kashe tsohon janar din soja da wani sarki kwanan nan, tare da umartar Ma’aikatar Ayyuka ta tarayya da ta fara gyaran hanyar Idofian–Omu-Aran–Eruku–Egbe–Kabba domin dakile yadda ’yan bindiga ke tserewa cikin sauki.

A yayin zaman da KAKAKI24 ta bibiya, Majalisar ta ce garkuwa da mutane ya koma sahun manyan laifukan ta’addanci da ke bukatar hukunci mafi tsanani, inda wasu sanatoci suka ce dole ne hukuncin kisa ya tabbata ba tare da bawa alkali damar ya rage shi ba. Majalisar ta kuma bukaci Shugaba Bola Tinubu ya kara gyara tsarin tsaro, duk da gargadin Sanata Ali Ndume cewa kalaman ka iya fassaruwa ta daban bayan tabbatar da sabbin hafsoshin tsaro. A wani mataki mai ban mamaki, an rusa Kwamitocin Tsaro da Leken Asiri da na Sojin Sama na Majalisar tare da bukatar sauran kwamitoci masu alaka da tsaro su gabatar da rahoton aikinsu cikin mako guda. Haka kuma an bukaci gwamnati ta karfafa kungiyoyin sa kai da duba dokar mallakar bindiga domin bai wa kwararru damar kare kansu.

Zaman ya dauki zafi yayin da aka tattauna batun garkuwa da daliban Kebbi, hare-haren Niger da farmakin cocin Eruku, inda Sanata Ashiru ya bayyana cewa Majalisar ta damu matuka da lamarin tare da yin korafi kan rahoton cewa sojoji sun janye daga makarantar Kebbi kafin farmakin ’yan bindiga. Mataimakin Shugaban Majalisar, Barau Jibrin, ya bukaci a nemi taimakon kasashen waje, yayin da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya nuna damuwa kan zubar bayanan sirri da ke bai wa ’yan ta’adda damar kai hari duk da gargadi. Sanata Adams Oshiomhole ya bukaci a binciki wanda ya bayar da umarnin janye sojoji daga makarantar Kebbi, yana mai cewa ya kamata a gurfanar da shi kan laifin ta’addanci, lamarin da Majalisar ta amince da shi yayin da ta kara dagewa kan hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet