Connect with us

Featured

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Naɗin Sabbin Jakadu 3 Da Tinubu Ya Gabatar Mata

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da naɗin mutum uku na farko da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar domin zama jakadun Najeriya a ƙasashen waje. Sabbin jakadun da aka tabbatar da naɗin nasu su ne Aminu Muhammad Dalhatu daga Jihar Jigawa, Lateef Kayode Kolawole Are daga Jihar Ogun, da Emmanuel Ayodele Oke, CFR, daga Jihar Oyo.

 

Majalisar ta cimma wannan matsaya ne bayan duba rahoton Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Waje, wanda ya gudanar da tantancewar waɗanda aka gabatar a makon da ya gabata, inda aka gamsu da cancanta da ƙwarewarsu don wakiltar Najeriya a matakin diflomasiyya.

 

Sai dai duk da wannan amincewa, har yanzu akwai ragowar wasu jakadu 64 da Shugaba Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa tun ranar 26 ga Nuwamba, waɗanda aka tantance amma ba a kai ga tabbatar da naɗin nasu ba. Wannan shi ne jerin sunaye na farko na jakadu da Shugaban ƙasa ya miƙa wa Majalisar tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

 

 

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet