Featured
Tinubu Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matuƙar bakin cikin sa kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu da safiyar Alhamis yana da shekaru 101. A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban ƙasar ya bayyana marigayin a matsayin “tushen daraja da nagarta” wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi.
Tinubu ya ce rasuwar Sheikh Dahiru babban rashi ne ga iyalansa, mabiyansa da kuma Najeriya baki ɗaya. Ya tuna irin addu’o’i da goyon bayan da ya samu daga shehin malamin tun a lokacin da yake neman kujerar shugaban ƙasa a zaben 2023, inda ya bayyana shi a matsayin malaminsu, uban kowa, kuma jagoran da ke kira zuwa ga zaman lafiya da tsoron Allah.
Shugaba Tinubu ya yi ta’aziyya ga mabiyan Tijjaniyya a fadin ƙasa da ma kasashen waje, yana mai kira da su ci gaba da bin koyarwar Sheikh Dahiru ta zaman lafiya, kyautata mu’amala da kuma ƙara kusanci da Allah. Ya ce irin rayuwar marigayin abin koyi ce da ya kamata a girmama ta ta hanyar aiki da darussan da ya bari.
Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa irin wannan manyan malamai su ne ginshiƙan al’umma, don haka ya roƙi Allah ya jikan Sheikh Dahiru Bauchi, ya ba iyalansa da mabiyansa haƙurin jure wannan babban rashi. Ya kuma jaddada muhimmancin musulmi su ci gaba da zaman lafiya da haɗin kai kamar yadda marigayin ya rayu.