Featured
Amurka Ta Sha Alwashin Hana Duk Wani Mai Hannu a Kisan Kiristocin Najeriya Bizar Shiga Ƙasar

Gwamnatin Amurka ta gargadi cewa za ta saka takunkumai da hana bizar shiga ƙasar ga duk wanda ta samu da hannu a zargin yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Ministan Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ne ya bayyana haka a dandalin X, inda ya ce matakin martani ne kan tashin hankalin da ake zargin ana yi wa Kiristoci. Sai dai ya yi wannan ikirari ba tare da gabatar da wani takamaimen hujja ba.
Rubio ya ce Amurka na ɗaukar mataki kan kowace irin barazana ga ‘yancin yin addini a Najeriya da sauran sassan duniya. Ya bayyana cewa za a dakatar da bizar duk wanda aka tabbatar ya tsara ko ya bayar da umarni, ko ya ɗauki nauyin cin zarafin masu yin addini. Ya kara da cewa matakin zai shafi gwamnoni ko mutanen da ke zaluntar jama’a kan addininsu.
A cewar rahotanni da Kakaki24 ta tattara, wannan martani na Amurka ya zo ne bayan wani kwamatin Majalisar Wakilan Amurka ya fitar da rahoto a jiya Laraba. Rahoton ya ƙunshi korafe-korafe daga wasu ‘yan majalisa da ke nanata ikirarin cewa ana kashe Kiristoci da gangan a Najeriya. Wannan batu ya sake tayar da cece-kuce a fagen diflomasiyya.
Masu sharhi na ganin matakin na iya ƙara tsoma Amurka cikin batun tsaro da addini a Najeriya, musamman ganin cewa zargin bai zo da cikakkiyar shaida ba. Wasu kuma na ganin hakan na iya haifar da sabbin matsaloli a hulɗar Abuja da Washington. Dai-dai wannan lokaci, ba a sami wani martani kai tsaye daga gwamnatin Najeriya kan wannan barazana ba.