Featured
Kogi : DSS ta gurfanar da Wanda Ake Zargi Da Jagorantar Harin Ƴanbindiga a Coci

Hukumar Tsaro ta Ƙasa (DSS) ta gurfanar da Abdulmalik Abdulazeez Obadaki, wanda ake zargi da jagorantar harin bindiga da aka kai wa cocin Deeper Life Bible Church a Otite, kusa da Okene a Jihar Kogi, a gaban kotu. Harin, da ya auku da safiyar 7 ga Agusta, 2012, ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 19 yayin zaman karatun Littafi Mai Tsarki, bayan wasu ‘yan bindiga uku dauke da bindigogin AK-47 sun buɗe wuta kan masu ibada.
Rahotanni sun ce mutane 15 sun mutu nan take, yayin da huɗu suka rasu daga baya sakamakon raunukan da suka ji, tare da jikkatar wasu da dama. DSS ta bayyana cewa harin na da alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma bayan wannan hari Obadaki ya jagoranci wasu hare-haren fashi a bankuna a Uromi, Jihar Edo, inda aka kashe mutane tare da kwashe kuɗaɗe masu yawa.
Daga bisani jami’an tsaro sun kama Obadaki tare da tsare shi a Gidan Yari na Kuje, amma ya tsere a lokacin fasa gidan yarin Yuli 2022. DSS ta sake cafke shi a 15 ga Nuwamba, 2025, sannan aka gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume guda shida da suka shafi ta’addanci da tserewa daga tsarewa. Obadaki ya amsa laifi ne kawai kan tuhumar tserewa, yayin da kotu ta ɗage shari’ar zuwa 26 ga Janairu, 2026, tare da umarnin ya ci gaba da kasancewa a tsare a hannun DSS.