Featured
Wani Mai-gadi Ya Kashe Abokin Aikinsa a Harabar Gidan Gwamnatin Gombe

Wani ma’aikacin gadi, Shuaibu Adamu mai shekara 19, ya kashe abokin aikinsa Mallam Umar, wanda aka fi sani da Baba Usama, a harabar Gidan Gwamnatin Jihar Gombe.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 26 ga Disamba, inda marigayin ke aiki a matsayin mai kula da rijiyar burtsatse.
Rundunar ’yan sandan jihar ta ce an same shi kwance babu rai, inda aka ɗaure shi da wando a wuyansa, tare da saka wani kayan maye a bakinsa. An garzaya da shi Asibitin Kwararru na Gombe, amma likita ya tabbatar da mutuwarsa, sannan aka ajiye gawarsa a dakin ajiya domin bincike.
Binciken farko da duba faifan CCTV ya nuna Shuaibu Adamu yana dukansa kafin mutuwarsa, sannan ya tsere daga wurin. Daga bisani ’yan sanda sun cafke shi a Bagadaza Quarters da misalin ƙarfe 11 na dare, inda ya amsa laifin, kuma har yanzu yana tsare yayin da ake ci gaba da bincike domin gurfanar da shi gaban kotu.