Featured
Bamu Tsara Jadawalin Zaɓen 2027 Ba – INEC

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ba ta fitar da jadawalin da tsarin ayyukan zaɓen shekarar 2027 ba, sabanin wasu rahotanni da ke yawo a wasu wurare. Hukumar ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya kuma mai cike da ruɗani.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban INEC, Adedayo Oketola, ya sanya wa hannu, hukumar ta jaddada cewa tana aiki ne bisa tanadin doka. Ta ce Sashe na 28(1) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya tanadi cewa dole ne INEC ta sanar da zaɓe aƙalla kwanaki 360 kafin ranar zaɓen gama-gari.
INEC ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa za ta fitar da sahihin jadawalin zaɓen 2027 a kan lokaci, bisa kundin tsarin mulki da Dokar Zaɓe. Hukumar ta kuma buƙaci jama’a da kafafen yaɗa labarai su yi watsi da rahotannin ƙarya, su dogara kawai da hanyoyinta na hukuma don samun sahihani.