Featured
Ƴan Bindiga Sun Nemi Naira Miliyan 29 Don Sakin Masu Ibada 166 a Kaduna

Iyalan Kiristoci 166 da aka sace a ƙauyen Kurmin Wali da ke Kudancin Kaduna sun ce ’yan bindiga sun nemi kuɗin N28.9m a matsayin kudin ajiyar babura 17.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai hari kan coci-coci uku a ranar Lahadi, inda suka sace mutane 177 kafin 11 daga cikinsu su tsere.
An bayyana cewa wannan shi ne hari na biyu da aka kai yankin cikin mako guda, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin mazauna yankin.