Featured
Matashi Ya Rasu a Ƙoƙarin Ceto Akuya Daga Rijiya

Hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo ta tabbatar da mutuwar wani mutum mai shekara 30, Shina Adedeji, da kuma wani mutum mai kimanin shekara 45 a wurare daban-daban na jihar. An gano cewa ɗaya daga cikin mutanen ya mutu ne yayin da yake ƙoƙarin ceto akuya daga cikin wata rijiya mai zurfi.
Mai ba Gwamna Seyi Makinde shawara kan gyaran harkokin kashe gobara, Moroof Akinwande, ya ce lamarin farko ya faru ne a yankin Mokola da ke Saki a ranar Litinin. A cewarsa, mutumin ya shiga rijiyar ne domin ceto akuya, inda ya makale a ciki kafin jami’an kashe gobara su iso su fitar da gawarsa.
A wani lamari daban a Ogbomoso, Akinwande ya ce Shina Adedeji ya faɗa cikin rijiya a yankin Aaje Ikose yayin da yake ƙoƙarin ciro wani abu. Ya gargadi al’umma da su fifita kiyaye rayukansu, yana mai jaddada cewa rayuwa ba ta da madadi.