Connect with us

Featured

Majalisar Ƙoli Kan Shari’ar Musulunci Ta Nanata Buƙatar Tsige Shugaban INEC

Majalisar ƙoli kan harkokin shari’ar musulunci a Najeriya (SCSN) ta sake nanata kiranta da a tsige shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, tana mai cewa ba zai iya yin adalci a babban zaɓen da ke tafe ba. Majalisar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sakatare-janar ɗinta, Nafi’u Baba Ahmad, ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce kiran ba shi da alaƙa da addini ko ƙabilanci, illa batun nagarta da inganci. Ta bayyana cewa sabuwar takardar ƙarin bayani ce kan wadda ta fitar a baya a ranar 28 ga Janairu, wadda ta ce an canja mata fassara, lamarin da ya sa ta sake fayyace matsayarta.

Majalisar ta zargi Farfesa Amupitan da rubuta wata takarda a 2020 da ta ƙunshi kalamai masu cin zarafi ga musulman Najeriya da arewa, tare da alaƙanta matsalar tsaro da jihadin Usman Ɗanfodio. Ta ce bai nesanta kansa da takardar ba har yanzu, tana mai jaddada cewa shugabantar hukumar zaɓe na buƙatar mutum mai kauce wa nuna bambancin addini da ƙabilanci.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet