Featured
Muna Neman Afuwar Ƙasashen Da Ke Makwabtaka Da Mu Kan Hare-haren da Muka Kai Musu – Shugaban Iran
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya nemi afuwar kasashen makwabta kan hare-haren da kasarsa ta kai musu a baya-bayan nan. A cikin wani sakon bidiyo da aka watsa a gidan talabijin na kasar, ya ce ya zama wajibi Iran ta nemi afuwar kasashen da hare-haren suka shafa.
Pezeshkian ya jaddada cewa Iran ba ta da niyyar kai hari kan kasashen makwabtanta. Ya ce gwamnatin kasar ta bai wa sojojinta umarni cewa daga yanzu kada su sake kai hari ga wata kasa makwabciya sai idan ita ce ta fara kai hari kan Iran.
Wannan na zuwa ne bayan da Iran ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya a matsayin martani ga hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai kan Iran, inda aka kashe jagoran addinin kasar. Shugaban ya kuma gargadi duk wanda ke tunanin amfani da wannan lokaci wajen kai wa Iran hari cewa kasarsa ba za ta lamunci hakan ba.
