Featured
Tinubu Ya Naɗa Farfesa Shegun Aina a matsayin Sabon Shugaban JAMB

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Farfesa Segun Aina a matsayin sabon shugaban hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i ta JAMB.
Farfesa Aina mai shekaru 39 ya maye gurbin Farfesa Is-haq Oloyede, wanda wa’adinsa a matsayin shugaban hukumar zai kare a ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2026.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya bayyana Aina a matsayin ƙwararren masani mai gogewa a harkokin jarrabawa, fasahar intanet da kuma sauye-sauyen da suka shafi al’umma.