Featured
Gwamnonin APC Masu Neman Tazarce Sun Ce Tinubu Ne Mafita Ga Ƴan Najeriya a 2027
Gwamnonin jam’iyyar APC da ke nneman wa’adi na biyu a jihohinsu sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takara a wa’adi na biyu a 2027. Sun ce sun yanke wannan matsaya ne bayan taron da suka gudanar a jihar Kebbi.
Gwamnonin sun bayyana cewa goyon bayan nasu ya samo asali ne daga bukatar ci gaba da manufofin gwamnati, gyaran tattalin arziki da kuma tabbatar da dorewar sauye-sauyen da ake yi. Sun amince cewa ‘yan Najeriya na fuskantar matsin rayuwa, amma suka ce sauye-sauyen gwamnatin Tinubu suna da muhimmanci domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.
Haka kuma, gwamnonin sun yi Allah wadai da matsalar tsaro da hare-haren sace mutane, tare da alƙawarin ƙara haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya wajen magance su. Sun kuma ce za su mayar da hankali kan noma, ilimi, lafiya, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’umma, tare da neman tazarce bisa ayyukan da suka gudanar, ba wai farfaganda ba.
