Featured
Zaben 2027 : Atiku Ya Sha Alwashin Tura Wa Ƙananan Hukumomi Kuɗaɗensu Kai Tsaye Idan Ya Zama Shugaban Nijeriya

Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi alkawarin cewa zai tabbatar da tura kuɗaɗen da aka ware wa ƙananan hukumomi kai tsaye zuwa asusunsu idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Barista Kenneth Okonkwo, ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, 1 ga Satumbar 2026.
Read Also : ’Yan Bindiga Sun Sace Shugaban APC a Karamar Hukumar Rogo
Ya ce gwamnatin da zai jagoranta za ta mutunta hukuncin kotu da doka, tare da kare ’yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi da sauran matakan gwamnati.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce tsarin zai taimaka wajen tabbatar da cewa kuɗaɗen jama’a sun isa ga hukumomin da aka ware musu, tare da ƙarfafa gudanar da mulki da ci gaba a matakin ƙasa.