Connect with us

Featured

Zan mayar da mafi ƙarancin albashi Naira 500,000 idan na zama shugaban ƙasa – Sowore

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, ya yi alkawarin mayar da mafi ƙarancin albashi zuwa Naira 500,000 a duk wata ga ma’aikatan Nijeriya idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Sowore ya kuma yi alkawarin samar da wutar lantarki na tsawon awanni 24 a kowacce rana, tare da tabbatar da samun ilimi kyauta kuma mai sauƙin samu a dukkan matakai. Ya ce gwamnatinsa za ta gina gidaje miliyan ɗaya na jama’a tare da yin garambawul ga dokokin haya domin rage wa ma’aikata wahalar biyan kuɗin haya na shekara ɗaya ko biyu a gaba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sowore ya bayyana waɗannan tsare-tsare ne a wata hira da jaridar Independent, wadda aka wallafa ranar Lahadi.

Read Also : Babu gudu ba ja da baya kan batun cire tallafin man fetur – Fadar Shugaban Kasa 

Ɗan takarar ya ce za a mai da kiwon lafiya haƙƙin kowane ɗan ƙasa, tare da bunƙasa masana’antu da noma, da sake gina ababen more rayuwa. Ya kuma yi alkawarin gyara harkokin tsaro, inganta jin daɗin jami’an tsaro da kuma amfani da fasahohin zamani wajen yaƙi da rashin tsaro.

Sowore, wanda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cikin ’yan takarar shugaban ƙasa 18 na 2027, ya ce AAC za ta gudanar da kamfen ɗinta daga tushe. Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar za ta dogara da tallafin jama’a wajen gudanar da kamfen, ba attajirai ko iyayen gida a siyasa ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet