Featured
ADC da NDC ba za su kai labari a zaɓen 2027 ba – Nentawe

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce jam’iyyun ADC da NDC ba su zama barazana ga APC a zaɓen 2027 ba. Ya bayyana hakan ne a Maiduguri bayan kammala taron jam’iyyar na kwanaki uku.
Nentawe ya ce APC ta lashe huɗu daga cikin zaɓukan cike gurbi biyar da aka gudanar a baya-bayan nan. Ya kuma yi nuni da zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ganye, Jihar Adamawa, inda ya ce APC ta yi nasara a ƙaramar hukumar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya fito. Nentawe ya ce hakan na nuna cewa jam’iyyar ta yi ƙarfi a ƙasa.
Read Also : NAWOJ Kano Commends AKCILS for Producing Quality Media Professionals
Shugaban APC ya ce sakamakon zaɓukan ya nuna cewa jam’iyyar tana da ƙarfi kuma ta shirya domin tunkarar zaɓen 2027. A yayin taron, shugabannin jam’iyyar sun kuma duba tsarin APC daga matakin ƙasa har zuwa rumfunan zaɓe.
Taron ya yanke shawarar ƙarfafa sulhu da haɗin kan ’ya’yan jam’iyya tare da inganta ayyukan yaƙin neman zaɓe. Haka kuma, shugabannin sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu, Mataimakin Shugaba Kashim Shettima da sauran ’yan takarar APC.
Pingback: NECO 2026: Kano ta zo ta farko a yawan ɗaliban da suka yi nasara a jarabawar NECO - KAKAKI 24