Featured
Gwamnatin Tarayya na shirin ciyo sabon bashin dala biliyan $1.5 daga Bankin Duniya
Gwamnatin Nijeriya ta fara tattaunawa da Bankin Duniya don ciyo sabbin basuka uku, waɗanda jimillarsu ta kai Dala biliyan 1.5.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan na zuwa ne, daidai lokacin da rahotanni suka tabbatar da cewa yawan bashin da ake bin Nijeriya ya kai Naira tiriliyan 166.79 a karshen watan Yunin 2026.
Rancen zai kunshi dala miliyan 500 kowanne, domin ayyukan jure sauyin yanayi, tallafin zamantakewa da bunƙasa yara ƙanana.
Na farko shi ne ƙarin dala miliyan 500 ga shirin ACReSAL, wanda ke yaƙi da zaizayar ƙasa, ambaliyar ruwa, ƙarancin ruwa da matsalolin noma. Idan aka amince da sabon rancen, jimillar kuɗin shirin zai tashi daga dala miliyan 700 zuwa dala biliyan 1.2, kuma ana sa ran Bankin Duniya zai duba batun a ranar 29 ga Oktoba 2026.
Read Also : NECO 2026: Kano ta zo ta farko a yawan ɗaliban da suka yi nasara a jarabawar NECO
Rancen na biyu na dala miliyan 500 zai tafi ne ga shirin HOPE-SP, domin samar da tallafin kuɗi ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi, da kuma inganta tsarin rajistar masu cin gajiyar tallafin. Na uku kuma dala miliyan 500 ne domin shirin bunƙasa yara tun daga haihuwa zuwa shekara biyar, wanda zai shafi dukkan jihohin Najeriya da Abuja, tare da mayar da hankali kan lafiya, abinci mai gina jiki, ilimi da tsaftar muhalli.
A gefe guda, bayanan Ofishin Kula da Bashin Ƙasa sun nuna cewa bashin Najeriya ya ƙaru daga Naira tiriliyan 152.40 a Yunin 2025 zuwa Naira tiriliyan 166.79 a Yunin 2026. Haka kuma, bashin Najeriya ga ƙungiyar Bankin Duniya ya kai dala biliyan 20.73.
