Featured
Ba zan iya zuwa yaƙin neman zaɓe kowacce jiha ba – Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce ba zai iya raka kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC zuwa dukkan jihohin Najeriya domin neman masa ƙuri’a a zaɓen 2027 ba.
Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja, yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC. Ya buƙaci mambobin kwamitin su isar da saƙon jam’iyyar ga ’yan Najeriya a faɗin ƙasar.
Read Also : Dangote Cement Hosts 2026 Football Tournament To Promote Inter-Community Unity
Ya ce ba ya son harkokin yaƙin neman zaɓe su ɗauke hankalinsa daga gudanar da gwamnati, yana mai cewa Najeriya na buƙatar kulawarsa a wannan lokaci.
Tinubu ya ce yana son gwamnatinsa ta jawo masu zuba jari zuwa Najeriya domin inganta tattalin arzikin ƙasar. Ya ƙara da cewa burinsa shi ne masu zuba jari su zo su zauna tare da saka kuɗaɗensu domin amfanin jama’a da makomar al’umma.
Pingback: Arc. Aminu Dabo ya fice daga jam'iyyar APC - KAKAKI 24