Featured
Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙudirin kafa yansandan jihohi

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da kudirin dokar da zai bai wa gwamnatin jihar damar kafa rundunar ’yan sandan jiha.
Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala, ya ce matakin ya biyo bayan amincewa da gyare-gyaren da Majalisar Wakilai ta yi domin sauƙaƙa kafa ’yan sandan jihohi a faɗin Najeriya.
Read Also : NUJ Yobe Inaugurates Five-Man Electoral Committee for 2026 Council Election
Haka kuma, majalisar ta amince da buƙatar Gwamna Abba Kabir Yusuf na rage kasafin kuɗin jihar na shekarar 2026, sakamakon sauyin kuɗaɗen shigar gwamnati. An rage kasafin daga Naira tiriliyan 1.477 zuwa Naira tiriliyan 1.222.
Majalisar ta ce raguwar kuɗaɗen da jihar ke samu daga Gwamnatin Tarayya, sakamakon sauye-sauyen dokokin haraji, ta tilasta sake duba kasafin. An ce matakin zai taimaka wajen daidaita kashe kuɗaɗen gwamnati da kuɗaɗen shigar da ake sa ran jihar za ta samu.
Pingback: Kotu ta umarci INEC ta cire sunan Uzodinma tare da sanya Rochas a matsayin ɗan takarar Sanatan Imo ta Yamma - KAKAKI 24