Featured
Zaɓen 2027 : Atiku Ya Yi Alkawarin Kawo Karshen Matsalar Tsaro Idan Ya Zama Shugaban Ƙasa
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin kawo ƙarshen matsalar tsaro, dawo da fata a zukatan ’yan Najeriya tare da sauƙaƙa tsadar rayuwa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya bayyana hakan ne ranar Laraba a jihar Sakkwato, yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar.
Read Also : Bincike: Gwamnan Kano ya buƙaci a sauya masa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya ce ’yan Najeriya sun gaji da yunwa, rashin tsaro da kuma alkawuran da ba a cika ba. Ya ƙara da cewa yaƙin neman zaɓensa wata dama ce ta sauya shugabanci.
Ya kuma bayyana cewa ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen a Sakkwato shi ne farkon tafiyar ceto Najeriya, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa ADC za ta lashe zaɓen 2027.
