Siyasa
Jam’iyyar APC za ta fara sayar da fom yau Talata

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ce, za ta fara sayar da fom ɗin na gani ina so ga masu sha’awar tsayawa takarar muƙamai daban-daban gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar a yau Talata.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa Mista Felix Morka, ne ya tabbatar wa manema labarai batun fara sayarwar jiya Litinin yana mai cewa za a fara sayar da fom a yau.
A cewar sa, “A gobe Talata ne za mu fara siyarwa. Ba da daɗewa ba za a fitar da ƙa’idodin yadda tsarin ayyukan mu zai gudana a kafofin mu na sada zumanta, Yayin da za a sayar da fom ɗin majalisun dokokin jiha a matakin jiha a faɗin kasa, sauran kuma za a sayar da su a nan Sakatariyar kasa.”
Tun da fari dai jam’iyyar ta sanya ranar Asabar ɗin da ta gabata a matsayin ranar fara sayarwar, sai dai daga bisani ta canja zuwa yau sakamakon gazawar da ɗan kwangila ya yi wajen kai fam ɗin.
A kan haka ne, kwamitin ayyuka na jam’iyyar NWC ya umurci sakatarorin jihohi 36 da su karɓi fom ɗin daga hannun ƴan takarar da ke neman kujerar majalisun dokokin jiha.
Hakan dai na daga cikin ƙoƙarin da jam’iyya mai mulki ta yi na ganin ta cika jadawalin ayyuka da kuma jadawalin hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC.