Labarai
Shugaban Kasa Ba Zai Tsoma Baki Kan Zaɓen Da Aka Yi Ba – Hadimin Buhari

Guda daga cikin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmad, ya jaddada cewa shugaban nasa ba zai tsoma baki a harkokin zaben dake gudana yanzu haka ba.
Ahmad ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga wata sanarwa da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya fitar.
Obasanjo ya yi kira ga Buhari da ya dauki matakan gaggawa don magance tashe-tashen hankula da suka biyo bayan zargin sabani a sakamakon zabe.
Ya kuma yi kira da a soke zaben da kuma sake gudanar da zabe a wuraren da aka samu hatsaniya.
“Don haka Cif Olusegun Obasanjo yana son shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi mana katsalandan a harkokin zaben mu, wanda shi kuma hakan ba zai iya aiwatarwa ba.”
Ya kan kyale irin wadannan cibiyoyi ko hukumomin su yi aiki da kansu, a cewar Ahmad kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.