Connect with us

Featured

Hukumomin Saudiyya Sun Hana Mahajjata Sama Da 269,000 Shiga Ƙasar Waɗanda Basu Mallaki Katin Shaida Ba

Hukumomin Saudiyya sun hana mutane fiye da 269,000 shiga ƙasar, waɗanda ba su mallaki katin shaida ba, gabannin fara aikin Hajjin bana, kamar yadda AlArabiya da AP suka ruwaito a jiya Lahadi 01 ga Yunin 2025.

Wannan matakin ya biyo bayan ƙoƙarin da ake wajen ganin an rage cunkoso, tare da tabbatar da tsaro yayin ibadar aikin hajjin na wannan wannan shekara.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta bayyana cewa wannan matakin ya shafi ƴan kasar waje da kuma mazauna kasar Saudiyya da ke ƙoƙarin gudanar da aikin Hajji ba tare da izini ba.

Ƙa’idojin da aka tsara su ne, dole sai waɗanda ke da izini ne kawai za su iya gudanar da aikin Hajji, ko da kuwa a Saudiyya su ke da zama din-din-din.

Wannan tsauraran matakai sun biyo bayan tasirin da maniyyatan da ba su da izinin shiga zai iya haifarwa ga lafiyar masu ƙoƙarin sauke faralli.

Majijoyin gwamnati sun gano cewa, a shekarar da ta gabata yawancin waɗanda su ka mutu sakamakon tsananin zafi mutane ne wadanda basu mallaki shaidar shiga garin na Mecca ba.

A halin yanzu, akwai kusan maniyyata 1.4 miliyan da ke da izini a Mecca, kuma ana sa ran karin maniyyata za su shiga kasar nan da kwanaki masu zuwa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet