Connect with us

Featured

Amurka Ta Rage Wa’adin Izinin Shiga Ƙasar (VISA) Ga Ƴan Najeriya Zuwa Watanni Uku

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da sabuwar doka dangane da bizar da ba ta dindindin ba ga ‘yan Najeriya.

A cewar wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka ya fitar a Abuja a ranar Talata 08 ga Yuli, “Yawancin bizar da ba ta dindindin ba da kuma waɗanda ba na diflomasiyya ba da ake bayarwa ga ‘yan Najeriya za su kasance na shiga sau ɗaya kacal tare da ingancin watanni uku.”

Wannan sabon mataki ya fara aiki nan take.

Sai dai ofishin jakadancin ya fayyace cewa “dukan bizar da ba ta dindindin ba da aka bayar kafin ranar 8 ga Yuli, 2025, za su ci gaba da kasancewa da ingancinsu kamar yadda aka bayar tun farko.”

Sanarwar ta bayyana cewa wannan matakin ya kasance wani ɓangare na tsarin da Ma’aikatar ke aiwatarwa a duniya na daidaita sharuddan biza (visa reciprocity process), wanda ake cigaba da duba da sabuntawa akai-akai – ciki har da ƙara ko rage yawan izinin shiga ƙasa da kuma tsawon wa’adin ingancin biza.

Amurka ta bayyana dalilin da ya sa aka kawo wannan sauyi, tana mai cewa “sharuddan samun bizar Amurka an tsara su ne don kare sahihancin tsarin shige da fice na ƙasar.”

Har ila yau, ofishin jakadancin ya bayyana cewa “wadannan sharudda na biza sun dogara ne da ka’idojin tsaro da fasaha na duniya.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Ofishin jakadancin Amurka yana aiki tare da hukumomin Najeriya domin tabbatar da cika waɗannan sharudda.”

 

 

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet sssjojobet güvenlikjojobet güvenlikjojobetholiganbetholiganbetjojobetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetjojobet erişimgrandpashabetjojobetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişDeneme Bonusujojobetjojobetjojobet