Connect with us

Featured

Likitoci Sun Baiwa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Awa 24 A Biya Buƙatunsu Ko Su Tsunduma Yajin Aiki

Ƙungiyar Likitoci ta (NARD) ta sake baiwa gwamnatin tarayya wa’adin awanni 24 domin biyan buƙatun da ta jima tana nema, bayan karewar tsohon wa’adin kwana goma da ta ɗauka. Shugaban ƙungiyar, Dr. Tope Osundara, ya ce ko-da-yake gwamnati ta yi alƙawarin magance matsalolin, dole ne a ga aiki nan take.

A cikin sanarwar da suka fitar ranar 1 ga Satumba 2025, NARD ta buƙaci biyan kuɗin Medical Residency Training Fund (MRTF) na 2025, biya na watanni biyar da suka rage daga karin albashin CONMESS (25–35%), da sauran bashin albashi da ya daɗe. Haka kuma, suna neman biyan kuɗin kayan aiki na 2024, gaggawar biyan kuɗin ƙwararru, tare da dawo da amincewar hukumar MDCN ga takardun shaidar ƙwarewar likitoci daga West Africa.

Ƙungiyar ta kuma nemi a raba takardun membobinsu da National Postgraduate Medical College of Nigeria, aiwatar da tsarin albashin likitoci na 2024, magance matsalolin jin daɗin aiki a jihar Kaduna, da kuma tallafa wa likitocin da ke asibitin koyarwa na LAUTECH Ogbomoso. Sun jaddada cewa ba tare da waɗannan matakai ba, likitoci za su tsunduma yajin aiki cikin gaggawa.

Dr. Osundara ya ce fiye da likitoci 2,000 har yanzu ba su samu kuɗin MRTF ba. Ya gargadi cewa idan gwamnati ta kasa biyan su nan da yau (Alhamis), to gobe (Jumma’a) za su fara yajin aiki wanda zai iya durƙusar da aikin lafiya a manyan asibitocin ƙasar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantsekabetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetcasibommatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet