Connect with us

Featured

Wahalar Da Ƴan Najeriya Ke Sha Ta Zo Ƙarshe- Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa tsare-tsaren tattalin arziƙin gwamnatinsa sun fara kawo sakamakon canji mai kyau, yayin da ƙasar ke bikin cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai. A cikin jawabin da ya gabatarwa ƙasar a ranar Laraba 01 ga Oktoba.

Shugaban Ƙasar ya bayyana muhimman nasarori da aka samu tun bayan fara mulkinsa a watan Mayu 2023, ciki har da bunƙasar GDP zuwa kashi 4.23% a zangon biyu na shekarar 2025, raguwar hauhawar farashi zuwa kashi 20.12% – mafi ƙasa cikin shekaru uku, da kuma ƙaruwa a asusun ajiya na kuɗaɗen ƙasa zuwa dala biliyan 42. Tinubu ya ce cire tallafin man fetur da haɗa farashin dala sun kawar da cin hanci, kuma sun baiwa gwamnati damar zuba jari a ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi da tsaro.

A bangaren tsaro, Tinubu ya ce rundunonin tsaro suna samun nasarori kan ta’addanci da ta’addar IPOB/ESN a Kudu maso Gabas, Boko Haram a Arewa maso Gabas da kuma yan bindiga a Arewa maso Yamma. Ya bayyana cewa daruruwan al’ummomi sun samu zaman lafiya, yayin da dubban ‘yan gudun hijira suka koma gidajensu. Haka kuma ya bayyana sabbin shirye-shiryen noman zamani don rage tsadar abinci, da kuma muhimman ayyuka irin su titin bakin teku na Legas-Calabar da aikin jirgin ƙasa na gabas.

Tinubu ya jaddada muhimmancin matasa a ci gaban ƙasa, inda ya ambaci tallafin karatu ga sama da ɗalibai 500,000 ta hanyar Nigeria Education Loan Fund, da shirye-shiryen lamuni ga matasa kamar Credicorp da YouthCred. Ya kuma ce shirin iDICE na dala miliyan 600 zai ƙarfafa harkar kirkire-kirkire da fasahar zamani. Shugaban Ƙasar ya kammala da kira ga haɗin kai da kishin ƙasa, yana mai cewa: “Mu zama ƙasa mai ƙera kaya, ba mai saye kawai ba. Mu rungumi Made-in-Nigeria. Mu biya haraji, mu yi aiki tare, domin sabuwar Najeriya mai cike da fata ta riga ta fara wayewa.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet