Featured
Za a Rufe Duk Makarantun Da Ke Karɓar Kuɗin Da Ba Naira Ba – Minista

Ministan Bunƙasa Ma’adinai, Dr. Dele Alake, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta rufe dukkan makarantun da ke karɓar kuɗin da ba Naira ba a matsayin kudi makaranta. Ya bayyana haka ne a wajen bikin “Nigeria Gold Day” a taron makon hakar ma’adinai na kasa da kasa karo na 10 a Abuja. Alake ya bayyana cewa wannan dabi’a tana cikin manyan hanyoyin da ke karya darajar kuɗaɗen ƙasa, tare da haifar da matsin tattalin arziƙi da ƙara tsadar dala.
Ya ce ba daidai ba ne iyaye su riƙa biyan har fam dubu 10 ko dalar Amurka dubu 10 ga makarantu da ke cikin Najeriya, wanda hakan ke tilasta musu neman daloli a kasuwa, domin yin hakan yana ƙara ɗaga darajar kudin waje. Ya kwatanta lamarin da abin mamaki, yana cewa babu wata ƙasa da ke yarda a kafa makaranta a cikinta sannan a dinga karɓar kuɗin ƙasashen waje.
Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnati na ɗaukar matakai ta hanyar amfani da fasahohin zamani don rufe ɓarnar da ake yi a harkar darajar zinare a ƙasar. Ya ce shirin sayen zinare na ƙasa (National Gold Purchase Programme – NGPP) zai taimaka wajen ƙarfafa ajiyar kuɗin waje na Najeriya da kuma ƙarfafa Naira. Wannan shirin zai bai wa gwamnati damar sayen zinare daga ma’aikata ‘yan ƙanana kai tsaye da Naira, maimakon kashe daloli wajen shigo da shi daga waje.
A nata jawabin, Babbar Daraktar Asusun Bunƙasa Ma’adinai, Fatima Shinkafi, ta bayyana cewa sashen hakar zinare a Najeriya na samun ci gaba fiye da yadda ake gani a wasu ƙasashe. Ta yi kira ga masu saka jari da su duba damar da ke cikin arzikin zinaren Najeriya domin tallafa wa shirin gwamnati wajen mayar da ƙasar cibiyar masu hakar ma’adinai a duniya.