Connect with us

Featured

Gwamnan Kwara Ya Nemi Agajin Gwamnatin Tarayya Sakamakon Ƙaruwar Matsalar Tsaro a Jihar

Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukaci gaggawar turo karin jami’an tsaro zuwa garin Eruku, bayan harin da aka kai wa cocin Christ Apostolic Church Oke Isegun, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyu. Rahotanni sun ce faston cocin da wani mai ibada ne suka rasa rayukansu yayin da mahara suka bude wuta a lokacin shirye-shiryen taron ibada.

Gwamnan ya fitar da wata sanarwa ta bakin kakakinsa, Rafiu Ajakaye, inda ya yi Allah-wadai da harin, tare da kira ga hukumomin tsaro su kara tsaurara matakan kare jama’a, musamman a yankin karamar hukumar Ekiti. Ya ce gwamnati na tare da al’ummar Eruku da iyalan wadanda abin ya rutsa da su. Ya kuma gode wa Shugaba Bola Tinubu saboda tura karin sojoji 900 zuwa jihar, wanda ya ce hakan ya kawo sauki a wuraren da ake fama da tashe-tashen hankali.

Harin, wanda ya faru misalin karfe 6 na yammacin Talata, ya jefa al’umma cikin firgici, musamman kasancewar yankin na kusa da jihar Kogi. Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa jami’anta da kungiyar sa-kai sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar, lamarin da ya hana su aikata mummunan danyen aiki fiye da haka.

Kakakin rundunar ’yan sanda, Adetoun Ejire Adeyemi, ta ce an gano gawar mutum biyu bayan aikin bincike, yayin da dan sa-kai daya ya jikkata sakamakon harbin bindiga. Ta tabbatar wa al’umma cewa bincike na ci gaba domin kamo wadanda suka aikata laifin. Rahotanni sun nuna cewa yankin ya dade yana fuskantar matsalolin tsaro, duk da hadin gwiwar jami’an tsaro da vigilante wajen yaki da miyagun laifuka.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet